Saudiyya ta ƙaddamar da alkalan da za su hukunta masu laifi a yayin Hajji da Ummara

0
257

Kasar Saudiyya ta kaddamar da wani reshen shari’a da ke da alhakin gudanar da shari’o’in da su ka shafi ayyukan Hajji da Umrah, kamar yadda kafafen yada labarai na Saudiyya su ka ruwaito.

Babban Lauyan Masarautar, Saud bin Abdullah Al Mujib ne ya bude ofishin gabatar da kara da ke kusa da Masallacin Harami, wuri mafi tsarki na Musulunci, a Makka.

Masu gabatar da kara na aikin Hajji da Umrah sun kware wajen bayar da kariya ta adalci ga ayyukan ibada, mahajjata da daukar matakan shari’a kan laifukan da suka saba musu.

Haka kuma za ta tabbatar da cewa alhazan Hajji da Umrah sun samu ‘yancinsu da kuma kariya, in ji jaridar Okaz ta Saudiyya.

Jaridar ta nakalto Al Mujib yana jaddada wajabcin gaggauta bin diddigin shari’o’in da masu gabatar da kara na Hajji da Umrah za su gudanarwa da kuma aiwatar da matakan da suka dace na yaki da munanan ayyuka da suka shafi zaman lafiya da tsarkin wuraren da suka dace da tsarin ladabtarwa na shari’a da karfi aka bai wa masu gabatar da kara.

“An haramta duk wani nau’in laifukan da ake yi wa alhazai. Haka ma an haramta aikata Laifuka kan ayyukan ibada ko wurare masu tsarki,” inji shi.