Hajjin bana: Mun tanadar wa alhazanmu ƙayataccen masauki – Gombe

0
481

Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta jihar Gombe, Alh Saad Hassan ya tabbatar wa alhazan jihar na 2023 cewa hukumar ta yi musu tanadin masaukai masu kyau da zasu zauna a Makkah a lokacin aikin hajjin dake tafe.

Alh Saad ya shaidawa HAJJ REPORTERS hakan ne a yayin ziyarar gani-da-ido kan shirye-shirye da kayayyakin da aka tanadar wa alhazan jihar Gombe daga ɗan kwangilar da also baiwa aikin da ke unguwar Misfala Konkaria a kan titin Hijira a Makkah.

“Gidan da muka yi amfani da shi a shekarar da ta gabata an rushe shi tare da wasu otal-otal kuma mun yi aiki tukuru don ganin mun samar da wannan masaukin da ya dace da mahajjatan mu kuma za mu tabbatar da cewa alhazanmu sun ji dadin wadannan kayayyakin domin su samu damar gudanar da aikin hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.

Babban Sakataren ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya bisa namijin kokarinsa da goyon baya ga ayyukan hukumar.