In dai ba wani canji aka samu ba, a gobe Juma’a ne a ke sa ran Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, za ta sanar da tabbataccen kuɗin aikin Hajjin bana.
Wata majiya mai karfi a NAHCON ta shaidawa Hajj Reporters cewa hukumar na shiri na karshe wajen sanar da kudin aikin Hajjin na bana.
Sai dai kuma nahiyar ta tabbatarwa Hajj Reporters cewa in dai ba wani canji na gaggawa aka samu ba, farashin aiki km Hajjin bana zai kai Naira miliyan 3.3.
Ma’ajiyar ta ce tsadar kayayyaki da haihuwar farashi na ayyuka a Saudiya ne ya haifar da rashin farashin aikin Hajjin.
Maniyar ta kara da cewa, ” a bara, kuɗin kama masauki da Riyal 2000 ne amma ana kuɗin ya nuna sau biyu.
“a halin yanzu haka ma wasu jihohi ma Nijeriya na fama da wahalar samun masaukai a kusa da masallacin harami,” in ji majiyoyin.