Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Mayu za a fara jigilar alhazan Nijeriya zuwa kasa mai tsarki domin aikin Hajjin 2023.
Hassan ya bayyana hakan yayin sanar da farashin aikin Hajjin bana a shelkwatar NAHCON a Abuja a yau Juma’a.
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sanya 21 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a rufe karabar kuɗaɗen Hajji da ga hukumomin alhazai na jihohi ƙasar karkashin tsarin Adashin Gata na Hajji.