Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta sanar da tabbataccen adadin kudin aikin Hajjin 2023. Hukumar ta tantance kudin kujerar aikin Hajjin da Alhazan Najeriya za su biya a jimillar kudin da bai ƙarasa Naira miliyan uku ba.
Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan da ya ke sanar da farashin kudin a yau Juma’a a babban ofishin hukumar da ke Abuja, ya ce maniyyatan da su ka taso daga Yola da Maiduguri za su biya Naira miliyan 2,800,000, yayin da masu tashi daga wasu jihohin Arewa za su biya N2,919,000.00.
Shugaban ya kuma ce yankin kudancin Nijeriya na da nau’ukan farashin hajji guda shida, inda yai bayanin cewa maniyyatan jihar Edo za su biya miliyan N2,968,000.00, na Ekiti da Ondo za su biya miliyan N2,880,000.000.
Alhazan da su ka taso daga Cross River za su biya miliyan N2,943,000.00, na Osun kuma za su biya miliyan N2,983,000.00, yayin da maniyyatan jihohin Legas, Ogun da Oyo za su biya Naira miliyan N2,999,000.000.
Alhaji Hassan ya kuma sanar da cewa alhazan kudu maso kudu da maso gabas, za su biya N2,968,000.00.
Ya ce bambamcin farashin ya samo asali ne saboda bambancin farashin jirgin sama inda ya nuna cewa wasu wuraren sun fi kusa da Saudiyya.
Ya kuma ce hukumar, bayan ganawar gaggawa da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi sun amince cewa a yau za a rufe shafin yanar gizo na rajistar wadanda ke biyan kudin ta adashin gata na Hajji.
Ya kara da cewa taron ya amince da cewa dole ne dukkan maniyyatan da ke da niyyar kammala biyan kudin aikin Hajjinsu su cika kafin ranar 21 ga watan Afrilu.