Kano: Hukumar Alhazai ta bukaci maniyyata su cika kuɗin aikin Hajji ya kai miliyan 2.9 kafin 21 ga Afrilu

0
351

Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano ta yi kira ga maniyyata, musamman wadanda su ka biya kafin farko na kudin aikin Hajjin bana, da su cika kuɗin kafin 21 ga watan Afrilu.

Babban Sakataren hukumar, Muhammad Abba Dambatta ne ya yi kiran yayin zantawa da manema labarai a jiya Juma’a a Kano.

Ya yi kiran ne awannin kadan bayan Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta sanar da Naira miliyan 2.9 a matsayin kuɗin hakkin bana ga maniyyatan arewacin Nijeriya, inda ta sanya miliyan 2.8 ga ƴan kudancin ƙasar.

Dambatta ya kuma ce maniyata aikin hajjin bana zasu biya kuɗin kujera Naira Miliyan 2 da dubu dari tara da goma Sha tara, Inda yayi kira ga duk wadanda basu cika kudin ba da su hanzarta cikawa kafin ranar 21 ga wannan wata na afirilu domin ita ce ranar da za’a rufe karbar kuɗin kujerar aikin hajji a kasa baki daya

Danbatta ya ce tashin da dalar Amurka ta yi na daya daga cikin dalilan da su ka sanya tashin kudin aikin Hajjin.

Ya kuma kara da cewa batun sake ginin masaukan alhazai a kasa mai tsarki da hukumomin kasar ke yi, don inganta Jin dadi da walwalar alhazai bakin Allah, shima ya haifar da tsadar kudin aikin Hajjin na bana.