An sanya 21 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarshe ta biyan kuɗin Hajjin bana a Yobe

0
421

Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe ta sanya ranar Juma’a, 21 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za ta rufe karɓar kuɗin zuwa aikin Hajjin bana na Naira dubu N2,890,000, kamar yadda Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta sanar.

Shugaban hukumar, Alh Mai Aliyu Usman ne ya bayyana haka bayan taro da sauran jami’an hukumar.

A cewar sa, cika kuɗin Hajjin a kan lokaci zai baiwa hukumar damar yin tsare-tsaren tafiyar, duba da lokacin da aka sanya na fara diban alhazai zuwa kasa mai tsarki.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Suleiman Alh Sabo ya fitar, shugaban hukumar ya ce waɗanda su ka biya cikakken kuɗin su kafin cikar wa’adin su za a yi wa rijista.