Hajjin bana: Za mu hukunta duk jihar da ta ƙi aiwatar da sanarwar kuɗin aikin Hajji da mu ka yi — NAHCON

0
524

Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta ce za ta hukunta duk hukumar jin dadin alhazai ta jihar da ta gaza aiwatar da kudin da aka amince da shi na aikin hajjin 2023.

A wata sanarwa da Mousa Ubandawaki, mataimakin daraktan yada labarai na NAHCON ya fitar, ya bayyana cewa wasu jihohi sun fara karɓar kudin aikin Hajji daban da ‘’wanda jihohi da hukumar alhazai ta ƙasa su ka amince da shi tare kuma da amincewar gwamnati.

Ubandawaki ya bayyana a cikin sanarwar cewa: “Da farko dai jimillar kudin Hajji ya kasance wanda hukumar ta sanar a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 wanda ya gaza Naira miliyan uku (N3,000,000) da ya hada da kudaden hidimomi na kowane fanni na mahajjatan da ke karkashinsa. Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jiha da kuma Dala 800 na alawus na matafiya da za a raba wa alhazai.

‘’Yana da muhimmanci a yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare da juna cikin jituwa da kwanciyar hankali da lumana, ta yadda za mu guji duk wani mataki na cin zarafin Alhazai’’.

Ya kara da cewa za a hukunta duk jihar da ta canja tsarin farashin Hajji ta hanyar soke lasisin gudanar da aiki ko kuma a kwace kujerun aikin Hajjin 2023 da aka ba ta.