Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Gombe ta yi kira ga maniyyatan jihar da su gaggauta cika kuɗin aikin Hajjin su ya kai Naira miliyan 2,919 da ga nan zuwa ranar Talata, 18 ga watan Afrilu.
Wannan na kunshe a wata sanarwar da Alhaji Sa’adu Hassan, jami’i a hukumar ya fitar a jiya Litinin.
Hukumar, a sanarwar, ta gargadi maniyyatan cewa duk wanda ya gaza cika kuɗin nasa ya kai Naira miliyan 2,919 kafin 18 ga Afrilu, to kuwa za a sayar da kujerar sa ga masu buƙata.
Hakazalika hukumar ta sanar da ci gaba da gudanar da shirin bitar alhazai da ga bayan sallah da sati ɗaya.
“Hukumar kin dadin alhazai ta jihar Gombe na sanar da maniyyata Cewar an kayyade kudin Hajjin bana 2,919,000,00. Ana kira ga maniyyata da suyi gaggawar kammala biyan sauran kudadensu zuwa ranar talata 18/4/2023, wanda bai kammalaba za’a sayar da kujerarsa ga mabukata.
” Har ila yau kuma hukumar zata fara bitan maniyyata sati Daya bayan karamar Sallah a Arabic College Gombe. Allah yabada ikon biya amin. Sanarwar daga Alh. Sa’adu Hassan