Duk da tsadar kudin aikin hajji, wasu hukumomin jin dadin alhazai sun ce sun riga sun ƙarar da adadin kujerun aikin Hajji da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta ware musu
“A jihar Edo, kimanin maniyyata 350 ne suka biya kuɗin aikin Hajjin bana gaba daya ko kuma wani bangare,” in ji Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Edo, Sheikh Ibrahim Oyarekhua.
Ya ce hukumar na son adadin ya kai na maniyyata 400, inda ya ƙara da cewa, “Mun nemi karin gurbi guda 150, kuma a taron gaggawar da muka yi, mun gabatar da bukatar a hukumance ga shugaban NAHCON, kuma ya yi mana alkawarin zai duba wannan bukatar ta mu,”
Ibrahim Oyarekhua ya bukaci maniyyatan da suka riga su ka biya wani kaso na kudaden da su yi maza su cika a kan lokacin da aka kayyade domin su samu damar tafiya zuwa kasa mai tsarki.
Hakazalika, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, ya bayyana cewa hukumar za ta bukaci karin kujeru 500 na aikin hajjin bana.