Hajjin 2023: NAHCON ta sanya Azman Air ya yi jigilar alhazan Jigawa yayin da jihar ta biya biliyan 2.5 na Hajji

0
215

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta saka Naira Biliyan 2.5 a asusun Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) na kudin Hajjin 2023 na jihar.

Shugaban hukumar, Alhaji Umar Labbo, ya shaidawa manema labarai a Dutse ranar Juma’a cewa NAHCON ta ware kujeru 1,225 na Hajjin 2023.

Ya ce kowane mahajjaci a jihar zai biya Naira miliyan 2.9 a matsayin kudin aikin Hajji, kamar yadda NAHCON ta amince.

Labbo ya kara da cewa kashi 80 cikin 100 na kujerun da hukumar NAHCON ta baiwa jihar an ware su ne ga kananan hukumominta 27 domin sayar wa ga maniyyata.

Ya kuma ce hukumar ta zabi jirgin Azman Air domin ya yi jigilar alhazan jihar a bana.

Shugavak ya kuma bukaci duk wadanda har yanzu ba su kammala biyan kudin aikin Hajjin su ba da su cika kafin ranar 17 ga Afrilu.

Labbo ya kuma yabawa Gwamna Muhammad Badaru na Jigawa bisa goyon bayan da yake baiwa hukumar.