Saudiya ta saka na’urar nuna yanayi a masallatan Harami biyu masu tsarki

0
138

Ma’aikatar Kula da Yanayi ta Saudi Arebiya ta sanar da cewa ta saka na’urar nuna yanayin iska a masallatan Harami biyu na Makkah da Madina.

A sanarwar da ta wallafa a shafin ta na twitter, ma’aikatar ta ce an samu ci gaban ne a wani ɓangare na shirye-shiryen Hajjin bana, inda za a rika samun bayanai sahihai kan yanayin iska da kuma taimakawa wajen kula da yanayin.

Na’urorin, in ji ma’aikatar, za su rika kula da yanayin iska na zafi ko sanyi, hadari, yawan zubar ruwa, da kuma nuna ɓangaren da iska take taho wa.