A ranar Lahadi Allah Ya yi mata cikawa kamar yadda sanarwar da aka wallafa a zauren WhatsApp na Hukumar Alhazai ta jihar ta nuna.
Sanarwar ta nuna za a yi jana’izar marigayiyar ce da misalin ƙarfe 9 safiyar Litinin a BanZazzau kusa da Makarantar Firamare ta Zaria.
Da fatan Allah Ya gafarta mata, Ya sa Aljanna Firdausi makomarta.