Hajjin 2023: Jihar Nasarawa ta jaddada aniyarta na bai wa maniyyatan bara muhimmanci

0
340

Hukumar Alhazai ta Jihar Nasarawa ta jaddada aniyarta ta bai wa maniyyatan bara da ba su samu zuwa Hajji ba suka kuma zaɓi barin kuɗaɗensu a hannun hukumar don Hajjin bana, muhimmanci.

Sakataren hukumar, Malam Idris Ahmad Almakura, shi ne ya bayyana haka yayin ganawarsu da kodinetocin ƙananan hukumomi game da Hajji ranar Lahadi a Lafia, babban birnin jihar.

Almakura ya ce, hukumar NAHCON ta ware wa Jihar Nasarawa kujeru 1567 don Hajjin 2023, wanda a cewarsa kujerun sun gaza adadin maniyyatan da aka yi wa rijista bana a jihar.

Don haka ya ce hukumar alhazai ta jihar za ta yi rabon kujerun ta hanyar farawa da maniyyatan bara da ba su samu tafiya Hajji ba sannan suka zaɓi barin kuɗaɗensu a hannun hukumar.

Sakataren ya ƙara da cewa, ya zuwa ranar 21 ga Afrilu ake sa ran rufe karɓar rabin kuɗi, sai dai ya ce wa’adin bai shafi maniyyatan bara da suka bar kuɗinsu a hannun hukumar ba.

Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin bai wa hukumar damar yin shirye-shiryen Hajjin bana a kan kari.

Yayin taron nasu, Almakura ya gargaɗi jami’an hukumar da kodinetocin Hajji a jihar da su kiyaye kowane irin mugun hali, yana mai cewa duk wanda aka kama ya cuci maniyyaci zai gani a ƙoƙonsa.

Daga nan, Idris Almakura ya yaba wa Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, dangane da goyon bayan da hukumar ke samu daga gare shi a kowane lokaci.