Buhari ya karɓi baƙuncin sarakuna da malaman Nijeriya a Saudiyya

0
249

Shugaban Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin wasu sarakuna da malaman Nijeriya a ƙasar Saudiyya.

Baƙin nasa sun fito ne daga shiyyoyin siyasa shida da Nijeriya ke da su, kuma sun ziyarci shugaban ne don yin buɗe-baki tare.

Bayanin ziyarar na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Kakakin Shugaban, Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta nuna cewa a ƙarshen taron, Shugaba Buhari ya jaddada manufofin gwamnatinsa na bunƙasa dukkan sassan ƙasar nan ba tare da nuna bambanci ba.

Buhari ya bayyana fatansa kan cewar watan Ramadan da ake ciki ya zama silar ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai da kuma ƙara wa ‘yan ƙasa ƙwazon aiki tukuru don cigaban ƙasa tare da nuna kulawa ga mabuƙata.

Buhari ya yaba wa baƙin nasa bisa ziyarar da suka kai masa wadda ya bayyana a matsayin aba mai matukar muhimmanci.

Tawagar baƙin ta haɗa da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauransu.

Yayin da suke jawabi, sarakunan sun ce sai da haɗin kai ƙasa ke iya cimma buƙatunta.

A ɓangaren malamai kuwa, akwai Babban Limamin Aso Rock, Malam Abubakar Abdulwaheed Sulaiman da Sheikh Al-Kanawi Alhassan Ahmed da Dr Bashir Aliyu Umar, Muhammad Kamaluddeen Lemu da Nuruddeen Danesi Asunogie da Alhaji Abdulrasheed Adiatu da kuma Sheikh Haroun Ogbonnia Ajah.

Sauran su ne; Alhaji Ibrahim Kasuwar Magani da Farfesa Shehu Ahmed Sa’id Galadanchi, sai kuma Alhaji Bala Lau.

Haka nan, Buhari ya gana da Otaru na Auchi, Dr Aliru Highbred Momoh da Sarkin Lafia, Justice Sidi Mamman Bage da Sarkin Bauchi, Rilwan Adamu Sulaiman da Akadiri Saliu Momoh da Abdulfatah Chimaeze Emetumah da Fatima Ijeoma Emetumah da kuma Alhaji Isa Sanusi Bayero.

Yayin taron, an gabatar da addu’o’in zaman lafiya ga Nijeriya da fatan Allah Ya sa Shugaban ya kammala wa’adin mulkinsa cikin nasara da kuma fatan nasara ga gwamnati mai jiran gado.