Saudiyya ta fara karbar katunan hada-hadar kuɗi na dukkan kasashe don aikin Hajji da Umrah

0
177

Kasar Saudiyya ta sanar da cewa a yanzu za a karbi duk wani nau’in katin hada-hadar kuɗi na kasa da kasa don aikin Hajji da Umrah a kasar.

Wannan sabon ci gaban zai baiwa mahajjata damar yin amfani da katinan su don yin mu’amala iri-iri, da suka hada da siyayya, cin abinci, da kama masaukai.

Matakin na zuwa ne a matsayin wani bangare na kokarin da Masarautar ke yi na daidaita ayyukan Hajji da Umrah da samar da kwarewa ga masu ziyara.

Da wannan sabon ci gaba, alhazai ba za su damu da ɗaukar makudan kuɗi ko musayar kuɗi ba, waɗanda za su iya ɗaukar lokaci da wahala.

A farkon watan nan ne ma’aikatar Hajji da Umrah ta shawarci maniyyata da kada su taho da makudan kudi ko kayayyaki masu tsada da suka hada da Zinare, duwatsu masu daraja, da karafa masu daraja a lokacin da za su je kasar domin gudanar da aikin Ummara.

Bugu da kari, gwamnati ta bukaci mahajjata da su rika saukar da manhajojin banki daga shafukan yanar gizo, da gujewa raba bayanan asusun banki ko aika kudi ga ƴan damfara , da kuma yin watsi da sakonnin kar-ta-kwana daga hanyoyi marasa tushe.

Idan an samu wani yanayi na damfara, ana shawartar mahajjata da su sanar da ma’aikatar ko hukumomin da abin ya shafa.