Ma’aikatar Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta baiwa alhazan Ummara damar ziyartar ko wanne gari a faɗin ƙasar.
Sai dai kuma ta ce wajibin sharadin samun izinin aikin Umra ta bayan Ramadan na nan daram.
Mahajjatan da ke neman yin aikin Umrah na buƙatar neman izini daga manhajar Nusuk ko Tawakkalna, muddin ba su kamu da cutar Korona ba, ko kuma sun yi mu’amala da wanda ya kamu da cutar.
Ma’aikatar ta bayyana cewa mahajjatan Umrah za su iya tafiya tsakanin Makkah da Madina da kuma kewayen garuruwan Saudiyya idan su na bukata.
Idan dai ba a manta ba a baya ma’aikatar ta sanya ranar 10 ga watan Shawwal a matsayin ranar karshe ga mahajjatan cikin gida da za su biya kaso na uku kuma na karshe na kuɗin aikin Hajji.
Kaso na ƙarshe ya kai kashi 40% daga cikin kuɗin da aka ƙayyade kuma aka amince da shi a Hajjin bana.
Ma’aikatar ta ce za a tabbatar da matsayin ajiyar lokacin da aka kammala dukkan biyan kuɗaɗe a cikin lokutan da aka kayyade.