NAHCON ta baiwa hukumomin alhazai na jihohi awannin 48 su biya kuɗaɗen Hajjin bana

0
452

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya ba da ranar Juma’a, 28 ga watan Afrilu a matsayin wa’adin tura kudin aikin Hajjin 2023 daga hukumomin kula da jin dadin Alhazai na Jihohi.

Ya bayyana hakan ne a yau 26 ga Afrilu, 2023 yayin wata ganawa da shugabannin hukumomin jin dadin Alhazai na Jiha a hedikwatar Alhazai ta NAHCON, in ji Fatima Sanda Usara, Jami’ar Yada Labarai ta Hukumar a wata sanarwa da ta sanya wa hannu.

Ta ce taron dai an yi shi ne domin tattauna muhimman batutuwan da su ka shafi kudaden da maniyyata su ka biya domin tantance adadin wadanda za a yi wa rijistar zuwa aikin hajjin 2023 daga Najeriya.

Hakan zai ƙayyade zai nuna alkalumman da za a kulla yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama.

A cewar shugaban, hukumar za ta yi farin cikin yin aiki da duk wani kudi da aka saka mata a asusu kafin ranar Juma’a, sannan ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyin jigilar jirage zuwa Saudiyya a 2023 bisa ga wannan adadin.

Ya bayyana cewa ana sa ran kashi 50% na biyan dillalan jiragen sama bayan sanya hannu kan yarjejeniyar yayin da wani kashi 35% zai biyo baya bayan kawo jiragen da masu jigilar alhazai sa su yi.

Babban jami’in hukumar ta NAHCON ya koka da cewa dole ne a yi la’akari da cewa duk wasu tsare-tsare sun ta’allaka ne da adadin maniyyatan da aka tabbatar sun biyan kudin aikin Hajji kafin a kammala.

Idan dai ba a manta ba an tsawaita wa’adin biyan kudin Hajji a lokuta da dama tun daga watan Janairun 2023.

A wani labarin kuma, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga da Nazarin Laburare, Yarima Sheikh Suleman Momoh ya bayyana cewa za a gudanar da aikin tantance rukunin farko na ma’aikatan aikin Hajjin 2023 a gobe Alhamis 27 ga watan Mayu.

Horaswa da sauran shirye-shirye za su biyo baya bayan tabbatar da waɗanda aka zaɓa.