Gwamnan jihar Neja ya naɗa sabon shugaban hukumar alhazai

0
354

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya amince da nadin Muhammad Aliyu a matsayin sabon Babban Sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

A wata sanarwa da Ahmed Matane, sakataren gwamnatin jihar Neja ya fitar a yau Alhamis a Minna, ya ce nadin Aliyu kan wannan mukami ya zo ne bisa kwarewa, cancanta, gaskiya, kwazo da kuma kwarewar aiki ta shekara da shekaru.

A cewar sanarwar, “ana sa ran sabon sakataren zai yi aiki bisa bin tsarin aiki da manufofin da ke kunshe a cikin hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

Matane ya ce ana sa ran babban sakataren zai yi amfani da ilimi da basirarsa da kuma kwarewarsa wajen gudanar da aikinsa ta hanyar yin aiki tukuru don tabbatar da amanar da aka danƙa masa.

Ya taya shi murnar nadin tare da yi masa fatan samun nasara da jan gora a kan gudanar da ayyuka a ofishin sa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, Aliyu zai maye gurbin Maku Lapai a matsayin sabon babban sakataren  hukumar.