Hukumar alhazai ta Abuja za ta fara duba lafiyar maniyyata

0
200

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Abuja ta ce za ta fara duba lafiyar maniyyata aikin Hajjin 2023 da ga ranar 5 zuwa 7 ga watan Mayu.

Daraktan hukumar, Malam Abubakar Evuti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Malam Muhammad Aliyu ya fitar a jiya Talata a Abuja.

Evuti ya kuma bayyana cewa, za a gudanar da aikin yin alluran rigakafin korona ga dukkan maniyyatan daga ranar 15 ga watan Mayu zuwa 17 ga Mayu, 2023, bisa sharuddan tafiya zuwa kasar Saudiyya.

Ya shawarci alhazai da su tabbata sun yi duk wasu shirye-shirye da hukumar ta ware domin samun jagoranci mai kyau don samun gamsuwa da kudinsu da su ka biya.

Sai dai daraktan ya gargadi dukkan maniyyatan da har yanzu ba su dawo da fom din da suka kammala ba ko kuma su mika fasfo din su na kasa da kasa da su yi hakan.

Hakan a cewarsa, zai baiwa hukumar damar bin diddigin hanyoyin samun takardun balaguro cikin lokaci mai kyau kafin a fara jigilar alhazai zuwa Saudiyya.