Hajjin bana: Mutane dubu 10 ne ke neman gurabe 230 na ma’aikatan lafiyar da za su duba alhazai

0
361

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya bayyana cewa sama da mutane dubu 10,000 ne daga ma’aikatan lafiya ke son shiga tawagar likitocin Najeriya domin aikin hajjin 2023.

Alh Hassan ya ce guraben ma’aikatan lafiya 230 hukumar ta ware, amma mutane dubu 10 ne su ka nemi aikin.

Ya taya waɗanda su ka samu nasara murnar kasancewa daga cikin wadanda aka zaba, ya kuma umarce su da su dauki zaben a matsayin amana da Ubangiji ya dora musu.

Shugaban ya kuma gargadi ƴan tawagar ma’aikatan lafiyar, NMT da su mutunta ka’idoji da dokokin kasar mai masaukin baki, wato Masarautar Saudiyya da ba ta lamunta da saba doka.

Hakazalika, Prince Sheikh Suleman Momoh, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Yada Labarai, Kididdiga da Ayyukan Ajiye kundin bayanai (PRSLS), wanda ya zama shugaban kungiyar likitocin, ya bayyana cewa zaben mambobin ya biyo bayan tsarin zabe na gaskiya karkashin kulawar hukumar bisa sa idon membobi 12.

Don haka ya jaddada cewa duk wani memba da ba zai bi ka’idojin da aka gindaya ba, to ya ajiye aikin.

Sheikh Momoh ya sanar da cewa da zarar sun sanya hannu kan takardar karbar aiki, za a sa ran za su yi aiki kamar yadda aka tsara.

Sheikh Momoh ya bayyana cewa NAHCON ta baiwa kula da lafiyar alhazai matuƙar muhimmanci.