Hajjin bana: Alhazan Gombe za su biya kuɗin hadaya ta Bankin Jaiz — Babban Sakatare

0
1800

Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Gombe, Alhaji Sa’adu Hassan, ya bayyana cewa alhazan jihar za su biya kuɗin hadayar su ta Bankin Jaiz a yayin gudanar da aikin Hajjin bana.

Wata sanarwa da ga sashen yada labarai na hukumar ta ce Hassan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yiwa maniyyata jawabi a wajen bitar alhazai a yau Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ya kuma yi wa maniyyatan ƙarin haske kan yadda tsare-tsaren Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON dangane da kuɗin aikin Hajjin bana da kuma shirye-shiryen fara jigilar alhazai zuwa ƙasa mai tsarki.

“Haka nan yakuma tabbatar da cewar gwamnatin Alh. Muhammad Inuwa Yahya ta shirya tsaf don ganin an baiwa alhazan jahar mu ilmin aikin Hajji domin samun hajj MABRUR tun daga yau har ran tafiya da ranar dawowa da duk wani tanadi na ganin Alhazan Gombe sunyi aikin Hajji cikin nutsuwa farinciki da jin dadi.

“Daga karshe ya ja hankalin alhaza da su tabbatar suna halartar bita kullum ta awa uku daga karfe Tara na safe zuwa shabiyun ranar jumu’ace kawai ranar hutu.

“Ya kuma Yaba da godiya ga Malaman bitar da Yan Agaji bisaga jajircewarsu domin ganin komai Yana tafiya yadda hukumar ta tsara,” in ji sanarwar.