Rikicin Sudan: Ɗaruruwan alhazan Ummara sun maƙale a Saudiyya

0
233

Daruruwan alhazai da su ka je aikin Ummara a kasar Saudiyya sun maƙale a kasa mai tsarki biyo bayan rikicin kasar Sudan da ya yi sanadiyar kawo tsaiko a harkokin sufurin jiragen sama na kasuwanci, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin Daily Trust ya samu labarin cewa wadanda lamarin ya fi shafa su ne alhazan Ummara da subka bi ta jirgin kamfanin Badr Airline, wani jirgin kasar Sudan, wanda a baya-bayan nan ya dakatar da ayyukansa sakamakon yakin.

Idan za a iya tunawa dai an lalata jirage biyu ne mako daya da ya gabata a birnin Khartoum sakamakon yakin Sudan.

Sai dai kuma galibin alhazan da su ka yi amfani da wasu kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa kamar Qatar Airways da Egypt Air da dai sauransu, na komawa kasar a kan lokaci duk da cewa galibin kamfanonin jiragen na zagaye sararin samaniyar Sudan.

Yayin da wasu kamfanonin jiragen sama su ka yi zagaye ta sararin samaniyar Sudan don kare lafiyarsu, Badr Air ya dakatar da ayyukansa, inda ya bar fasinjojin da suka yi tafiya tare da shi a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Umrah.

Wani fasinja da ya makale, wanda ya zanta da wakilin Daily Trust a ya ce an bukaci wadanda suka bi ta jirgen Sudan da su nemi wasu jiragen domin komawa gida.

An kuma gano cewa wasu da suka bi ta wasu kamfanonin jiragen sama da ke zagaye wa ta sararin samaniyar sai sun biya ƙarin kudi kafin a dauko su zuw gida.