Duk da tsadar aikin Hajjin bana, kujeru 3,132 na Bauchi sun ƙare har ana nema

0
429

Kujerun aikin hajji 3,132 da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta baiwa jihar Bauchi sun ƙare ƙarƙaf, duk da tsadar kudin aikin hajjin na bana da ya kai N2,919,000.

Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Bauchi, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya bayyana haka a wani shiri na addini da rayuwa na gidan talabijin na NTA Bauchi, wanda ya gudana jiya Asabar 29 ga Afrilu, 2023.

A wata sanarwa da Muhammad Sani Yunusa Jami’in Yada Labarai na hukumar ya fitar a yau Lahadi, ya ce shirin talbijin din wani yunkuri ne na hukumar don sanar da al’umma halin da ake ciki kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2023.

Imam Abdurrahman ya ce “Ba mu da sauran gurbi na kujerun aikin hajji, amma mun mika bukatar ga hukumar alhazai ta kasa don neman kari wa maniyyatan mu”.

Ya alakanta tashin farashin hajjin bana da tsadar masaukai a kasar Saudiyya da kuma faduwar darajar Naira akan Dalar Amurka.

Da ya taɓo batun bita, Imam Abdurrahman ya ce ba a yin ibada cikin jahilci, inda ya kara da cewa neman ilimi ga musulmi don bashi damar gudanar da ayyukansa na ibada yadda ya kamata ya zama tilas.

Ya roki malaman bita a cibiyoyin bita da ke fadin jihar da su tallafawa maniyyata yadda ya kamata, inda ya kuma ja hankalin maniyyatan da su yi anfani da damarsu don sanin hukunce+hukuncen aikin Hajji.

Ya yi amfani da kafar sadarwar wajen nanata kudurin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na ganin jihar Bauchi ta ci gaba da rike sunanta a matsayin Wanda tayi fice wajen tallafawa alhazai.