Kamfanonin jiragen saman da aka zaɓa domin jigilar mahajjatan bana a Najeriya sun ƙi yarda su sa hannu a kan yarjejeniya da Hukumar Aikin Hajji ta ƙasar saboda rikicin Sudan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wakilan kamfanonin jiragen sun haɗa da na Air peace da Azman Air da Max Air da kuma Aero Contractors.
Tun farko an shirya kamfanonin za su rattaba hannu ne ranar Alhamis, amma yanzu an ɗage sai Talata mai zuwa, saboda wakilan kamfanonin sun nemi a ba su damar tattaunawa da shugabanninsu.
Sai dai jirgi ɗaya da zai yi aikin na ƙasar waje shi ne Fly Nas kuma tuni ya rattaba hannu, inda a yarjejeniyar aka amince zai yi jigilar maniyyata 28,000 kimanin kashi 40% na mahajjatan bana daga Najeriya.
Rufe sararin samaniyar Sudan saboda rikici, zai shafi jigilar aikin hajjin bana daga wasu ƙasashen Afirka, saboda ita ce hanya mafi gajarta zuwa Saudiyya.
Idan aka sake sabuwar yarjejeniya tsakanin Hukumar NAHCON da masu kamfanonin jiragen sama, akwai yiwuwar kuɗaɗen aikin hajjin za su ƙaru, a kuma sake nazari kan tsare-tsaren aikin Hajjin.
A watan Afrilu ne NAHCON ta ƙayyade mafi ƙarancin kuɗin da za a biya na aikin hajji daga naira miliyan 2.88 zuwa naira miliyan 2.9.