Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya biya kashi 65 cikin 100 ga kamfanunuwan sufurin jirgin sama don samun nasarar jigilar alhazan Nijeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da Hajjin bana.
Hajj Reporters ta rawaito cewa rikicin da ya barke a Sudan ya haifar da kulle sararin samaniyar ƙasar, inda ya sanya tafiya zuwa Saudiyya daga Nijeriya ta ƙara tsayi daga sa’o’i 4 zuwa sa’o’i 7.
Hakan ne ya sanya kamfanunuwan sufurin jiragen sama da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta amince su yi jigilar alhazai a bana su ka nemi a yi musu ƙarin kuɗin sufuri saboda tsawitar sa’o’in tafiyar da kuma haraje-haraje da za su biya a kasashe kusan biyar da za su keta kafin su isa Saudiyya.
Ko a ranar Alhamis ma, Hajj Reporters ta rawaito yadda kamfanunuwan su ka ƙi rattaba hannu a kan yarjejeniyar jigilar alhazai ta bana, in da suka nemi a yi musu ƙarin haraji sakamakon tsayin tafiyar da ya karu sakamakon rikicin Sudan.
Sai dai kuma a wata ganawa da masu ruwa da tsaki, shugaban NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya biya kashi 60 na harajin ga kamfanunuwan sufurin jiragen sama.
A wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yada Labarai, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta kuma bayyana cewa Buhari ya baiwa NNPCL umarnin samar da man jirgin sama ba tare da yanke wa ba domin a samu nasarar jigilar alhazan na bana.
Hakan na nufin ana sa ran kamfanunuwan sufurin jiragen sama na ƙasa guda hudu da sauka ƙi sanya hannu a yarjejeniyar, ka iya sanya hannu nan gaba kadan.
Sai dai kuma za su kara ganawa da NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki a ranar 9 ga watan Mayu don warware matsalolin.