Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Nasarawa, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar za su fara aikin allurar rigakafi da duba lafiyar maniyyatan Jihar na Hajjin 2023.
A gobe Laraba ,10 ga wata zuwa Lahadi 14 ga Mayu, 2023 za a gudanar da aikin tantancewar likitocin a shiyyar sanatoci uku, kamar yadda aka nuna a cikin shirin.
Wannan atisayen ya zama wajibi ga dukkan maniyyata saboda rashin gabatar da kansu don yin rigakafin da kuma tantancewar ka iya rasa damar gudanar da aikin Hajjin bana.
Ga wadanda ba za su samu damar zuwa wajen aikin ba ka iya zuwa shelkwatar hukumar da ke kan titin Jos a Lafia domin jami’an kiwon lafiya za su zauna don yi musu tantancewar.