Hajjin bana: Hukumar alhazai ta fara samar wa da maniyyata biza a Bauchi

0
227

A wani bangare na shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin bana, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Bauchi ta fara aikin samar da biza ga maniyyatan jihar.

Babban Sakataren hukumar, Imam Abdurrahman Ibrahim Idris ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa.

Imam Idris ya ce dukkan maniyyatan da su ka kammala biyan kudin aikin hajjin an sanya su a cikin tsarin samar da bizar.

Babban Sakataren, ya kuma bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta baiwa kamfanin Max Air aiki a hukumance na jihohi biyar ciki har da jihar Bauchi.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a fitar da jadawalin jigilar alhazai na bana, inda ya ce za a bayyana wasu muhimman bayanai bayan ganawar da suka yi a wannan mako a Abuja.

Akan allurar rigakafi da raba jakankunan alhazai kilo 32 da 8, Sakataren ya tabbatar da cewa hukumar ta kammala shirye-shiryen gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.

Da ya ke magana kan alhazan da ke karkashin shirin Adashin Gata na Aikin Hajji, Imam Idris, ya ce hukumar ta karbi sunayen maniyyata 154 da suka biya cikakken kudin tafiyarsu a karkashin shirin.