Hajjin bana: Kamfanonin jiragen sama sun sanya hannu a yarjejeniyar jigilar maniyyata

0
732

A karshe dai kamfanonin jiragen sama da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta zaɓa su yi jigilar alhazai na Hajjin bana sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar jigilar alhazan.

A tuna cewa a makon da ya gabata, kamfanonin sun ƙi sanya hannu a kan yarjejeniyar har sai an musu ƙarin kuɗaɗe sabo da tafiya zuwa Saudiyya ta ƙara tsayi da tsawon awanni 3 a sakamakon rikicin Sudan.

Amma daga baya sai gwamnatin Nijeriya ta shigaaganar, inda ta yi alkawarin biyan kashi 65 na kuɗin harajin da kamfanonin za su biya.

A yau Talata ne dai kamfanonin jirgin sama, da su ka haɗa da Azman, Max Air, Aero Contractors, Air Peace, Arik Air su ka rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazan.

Wannan ci gaba shi ne ya kawo karshen fargabar da maniyyatan ke yi wajen samun jinkirin tashin su zuwa kasa mai tsarki.