Hajjin bana: Kamfanin jiragen Saudiyya, Flynas ya karo manyan jirage 3

0
477

Kanfanin jiragen sama na Saudi Arebiya, Flynas ya karɓi manyan jirage guda uku daga cikin gida 120 da ya yi oda daga Amurka a kan kudi Dalar Amurka biliyan 10.

Jirage ukun sun hada da mai faɗin jiki A330 da kuma matsakaitan jiki A320 guda biyu, inda su ka zama ƙari a kan sabbin jirage 19 da su ka siyo a wannan shekara.

Jirage ukun sun sauka a Jeddah da Riyadh, inda a farkon watan nan, inda A320 din biyu su kasauka a filin jirgin sama na King Khalid a Riyadh, sannan A330 din ya sauka a filin jirgin sama na King Abdulaziz da ke Jeddah.

A halin yanzu kamfanin na da jirage 48, kashi 84 kenan a shekara biyu, idan aka kwatanta da guda 26 da kamfanin ya mallaka a watannin ukun farko na 2021.

A watanni 26 da suka gabata, Flynas ya karo jirage 22 kenan.