A ci gaba da shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin 2023, Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta shirya taron horaswa na yini daya kan kula da aikin hajji, wanda za a gudanar a dakin taro na gidan alhazai a ranar Asabar.
Shirin mai taken: ” Horo da Ƙarfafawa ga Shugabannin Hukumomi a aikin Hajji” ana sa ran babban darakta kuma mai ba da shawara kan harkokin Hajji da Umrah a Saudiyya, Dr. Badr Muhammad Al solamin zai gabatar da jawabi.
Sauran jami’an sun haɗa da: Dr. Mohammed Shokri Zamzami, Babban Darakta na Kwamitin Tawwaf na Alhazai da Jamrat Grouping a Muassassah, Abdullah Hammadu Adam, Jami’in Gudanarwa, Muassassah, in ji sanarwa daga Mousa Ubandawaki, Mataimakin Darakta, Yaɗa Labarai na NAHCON.
Sama da Jami’ai 90 ne ake sa ran za su halarci taron, wanda ya kunshi mambobi da shuwagabannin Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi, Manyan Jami’ai hukumomi Masu Zaman Kansu na Kasa da Kasa, Daraktoci da Ma’aikatan Gudanarwa na NAHCON da sauran masu ruwa da tsaki.
Jami’an, in ji sanarwar, sun iso Nijeriya ne bisa kyakkyawar tarbar daga Shugaban Hukumar NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan, Kwamishinan Kula da Ma’aikata da Kudi (PPMF), Alh. Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Watsa Labarai da Ayyukan Laburare (PRSILS), Sheikh Suleman Mommoh da Kwamishinan Ayyuka, Lasisi da Yawon shakatawa (OIL), Alh. Abdullahi Magaji Hardawa, da Babban Ma’aikatan Gudanarwa na Hukumar.