Rikicin Sudan ya janyo ƙara kuɗin aikin hajji bana a Najeriya

0
572

Hukumar alhazai ta Najeriya ta tabbatar da cewa yaƙin da ake yi a Sudan zai shafi jigilar mahajjatan ƙasar na bana.

Hakan kuma mai yiwuwa ne zai janyo a buƙaci maniyyata su biya ƙarin kuɗi.

A yau ne, hukumar da kamfanonin sufurin jiragen sama na cikin gida suka rattaba hannun a kan yarjejeniyar jigilar mahajjatan ta bana.

A makon jiya dai sun gaza yin hakan saboda batun ƙarin kuɗi.

Sai dai hukumar ba ta bayyana ko matakin na nufin, maniyyata aikin hajji ne za su biya ƙarin kuɗin da dogon zagayen zuwa Ƙasa mai Tsarki ko a’a ba.

Abdullahi Magaji Hardawa, kwamishinan kula da tsare-tsare da gudanar da aikin Hajji a hukumar ya ce kamfanonin sufurin jiragen sama sun nemi sai an daddale kafin sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Ya ce ba a cimma matsaya zuwa yanzu a kan ko mahajjata ne za su yi ƙarin kuɗin na jigilar aikin hajjin na bana ba.

A cewarsa, matuƙar ba a buɗe sararin samaniyar Sudan ba, har zuwa lokacin da aka fara jigilar mahajjatan bana daga Najeriya, hakan na nufin sai jiragen sama sun yi zagaye, abin da kuma tabbas zai haddasa ƙarin kuɗi.

Jami’in ya ce babban hatsari ne jirgin sama ya ce zai ratsa ta sararin samaniyar Sudan, abin da ya janyo su kansu hukumomin ƙasar suka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama ta sararin samaniyar Sudan ɗin.

Harɗawa ya ce matuƙar aka fara jigilar maniyyata aikin hajji na bana, ba tare da an bi ta samaniyar Sudan ba, za a fuskanci matsaloli guda biyu ko fiye.

“Na farko, in ba za a shiga ta sararin samaniyar Sudan ba, dole za a shiga ta wasu ƙasashe. To ƙasashen nan akasari, za a biya su kuɗin ratsawa ta sararin samaniyarsu.

To maimakon kuɗin da za a biya na ƙasa ɗaya, wato Sudan. (A yanzu) Mai yiwuwa a biya na ƙasashe da yawa. Kun ga an samu ƙarin kuɗaɗe kenan,” Abdullahi Harɗawa ya tabbatar.

Na biyu, a cewarsa, tun da akwai ƙarin tazara kamar na sa’a biyu a tafiyar jirgin sama, man da jirgin yake sha ma zai ƙaru kenan, lamarin da shi ma ke nufin ƙarin kuɗi game da batun jigilar alhazai.

Abdullahi Harɗawa ya ce kamfanonin sufurin jiragen sama sun sa hannu a kan yarjejeniyar jigilar aikin hajjin na bana ne bayan an daddale tsakaninsu da Hukumar kula da Aikin Hajji ta Ƙasa kan matsalolin da za a iya fuskanta.

Ya ce: “Sun amince sun sa hannu ɗin, amma an yarda akwai bukatar a san yadda za a yi, a ƙara musu farashi”.

Jami’in na hukumar aikin hajjin Najeriya ya ce sai dai shi maniyyaci ya riga ya biya kuɗi, “bisa yadda aka tallatar masa.

Don haka ba a cimma wannan matsayar ba tukunna”.

An tambayi Abdullahi Magaji Harɗawa ko hakan na nufin mai yiwuwa ko za a buƙaci maniyyaci ya biya ƙarin kuɗi? Sai dai ya ce zuwa yanzu, ba zai iya tabbatar da hakan ba.

“Amma dai abin da nake tabbatar miki shi ne, eh akwai bukatar ƙarin kuɗi. Akwai tazara da yawa. Akwai ɗawainiya da yawa. Ƙarin kuɗin nan daga ina zai fito? Shi ne ba a cimma matsaya ba”.

Kamfanonin sufurin jiragen saman da suka sa hannu kan yarjejeniyar sun haɗar da – Air Peace da Azman Air Services da Aero Contractor da kuma Max Air.
Source: BBC Hausa