Ƙarin kuɗin jirage: Sheikh Tijjani Kalarawi ya roƙi Buhari ya tallafawa maniyyatan Hajjin bana

0
446

Shararren malamin addinin Muslunci a Kano, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya tallafawa maniyyatan Nijeriya na Hajjin bana sakamakon ƙarin kuɗaɗe da ake tunanin za a samu sakamakon yaƙin Sudan.

Hajj Reporters Hausa ta rawaito cewa yakin da ake yi a Sudan ya sanya tafiya zuwa Saudi Arebiya ta ƙara tsayi da wajen sa’o’i uku, inda hakan ya sanya kamfanunuwan sufurin jiragen sama su ka nemi a yi musu ƙarin kuɗi domin guje wa samun faɗuwa duba da karin kuɗaɗen mai da biyan harajin sararin samaniyar ƙasashen da za su bi yayin jigilar alhazai.

Da ya ke zantawa da Rahma Radio a Kano, Sheikh Kalarawi ya roƙi Buhari da kada a saka maniyyata su sake biyan wani kuɗin bayan sun riga sun biya kudin Hajji mafi yawa a tarihin Nijeriya.

A cewar Kalarawi, shugaba Buhari ya taimaka ya tallafawa maniyyatan da su ka riga su ka biya kudaden su tunda dai kamfanonin jiragen sama sun nemi dole a yi musu kari sakamakon zagaye da za su yi zuwa Saudiyya, wanda yaƙin Sudan ya tilasta musu yin hakan.

“Kira na ke ga shugaba Buhari, a matsayin sa na shugaba jajirtacce mai kishin al’ummar sa da kuma addini. Ina kira da ma yan majalisun tarayya masu kishin addini da su shiga wannan lamari su kawo sauki ga mahajjata bakin Allah.

“Sun daure sun biya makudan kudade da wahala, amma wani lamari ya Kunno Kai daga kamfanonin jiragen sama saboda za su yi zagaye ta wasu ƙasashen ga shan mai saboda nisan zango.

“Shi ne na ke kira ga shugaban ƙasa da ya shiga lamarin domin a saukaka wa mahajjata,” in ji Kalarawi.