Maniyyata ba za su kara biyan kudi ba duk da karin dala 313 da aka samu a kan kudin Hajjin bana – NAHCON

0
472

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta bayyana cewa, duk da karin kudin aikin hajjin bana da kimanin Dalar Amurka 313 (N141, 476), hukumar ba za ta nemi maniyyatan ƙasar su sake biyan wasu kudade ba.

Shugaban Hukumar NAHCON, Zikirullah Kunle Hassan ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ya ke gabatar da jawabinsa na bude taron bita na yini daya ga jami’an Hajji da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta shirya a gidan Hajji da ke Abuja a yau Asaba.

Bayan barkewar rikici a Sudan da kuma rufe sararin samaniyarta, kamfanonin jiragen saman Najeriya hudu da aka zaba don aikin Hajjin 2023 sun bukaci hukumar da ta ƙara dala 250 na tikitin jirgin kowane mahajjaci.

Alhaji Hassan ya kuma ce hukumar a ranar 6 ga watan Mayu, ta gano cewa akwai karin cajin dalar Amurka 63 daga Saudiyya wanda ba a saka su ba a yarjejeniyar da aka yi tun farko kafin bayyana kudin tafiya na bana.

Ya ce tuni NAHCON ta rubutawa ma’aikatar Hajji, inda ta ja tunasar da ita kan karin da aka samu, inda ya kara da cewa, “muna fatan samun amsa mai kyau da ga gare su”.

Shugaban na NAHCON ya ci gaba da cewa hukumar ta yanke shawarar cewa ba za ta ɗorawa kowanne maniyyaci nauyin dake biyan wani kuɗi ba.

Alhaji Hassan ya ce a yanzu NAHCON ta zama hukuma mai cin gashin kanta, wacce ba ta karɓar wani tallafi daga gwamnati, maimakon haka ya ce hukumar na samar da kudaden shiga ga gwamnati.

“NAHCON ita kadai ke ɗaukar nauyin aikin Hajj,” in ji Alhaji Hassan.