Hajj 2023: Shugaban hukumar alhazai na Katsina ya ziyarci sarakunan Katsina da Daura

0
519

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Aminu Abdulmumini Usman tare da sauran membobin shi sun kai ziyarar ban-girma ga masu martaba Sarkin Katsina da Daura, Alhji Abdulmumini kabir Usman da Alhaji Umar faruq Umar.

Da ya ke jawabi a masarautun guda biyu, Shugaban Hukumar Alhaji Usman ya Shaida masu cewa sunzo ne domin neman tabarraki tare da addu’ar su akan wannan aiki da gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ya basu.

Shugaban yance shirye-shiryen hukumar ya yi nisa waje ganin aikin Hajjin bana yayi nasara.

Daga nan ya nemi shawara da addu’a ga sarakunan biyu domin samun sauke nauyin da aka ɗora musu.

A nasu jawabin Masu martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da na Daura, Alhji Umar Farouq Umar sun yi musu murna akan wannan zaɓar su.

Sun kuma ja kunnuwan su dasu ji tsoron Allah tare da jajircewa wajen gudanar da aikin su.