Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da cewa A Yau za ta fara aikin yi wa maniyyatan aikin hajjin bana gwaje-gwajen lafiya.
Mataimakiyar daraktan wayar da kai da ilimintarwa ta hukumar, Hadiza Abbas Sanusi ce ta bayyana hakan a wata sanarwa a yau Lahadi.
Ta ce za a gudanar da gwajin lafiyar a cibiyoyin kiwon lafiyar jihar daga ranar Litinin, 14 ga Mayu.
Ta sanar da cewa kowane mahajjaci ya karbi fom din gwajin lafiyarsa daga jami’in aikin Hajji a kananan hukumominsu inda su ka biya kudin aikin Hajjin.