Hajjin bana: Hajj Reporters Alkauthar Travels sun ƙaddamar da haɗin gwiwar aiki

0
592

HAJJ REPORTERS Media Limited, mawallafan www.hajjreporters.com da Mujallar Hajj Reporters sun ƙaddamar da kulla hadin gwiwa ALKAUTHAR TRAVELS & TOURS, kamfanin da ya samu lambar yabo domin kawo rahotanni kan aikin Hajjin 2023.

Wani bangare na yarjejeniyoyin da aka cimma sun hada da kawo cikakkun labarai kan dukkan ayyukan tafiye-tafiye da yawon bude ido na Alkauthar dangane da hidimomin da take yi wa dukkan maniyyatan da ke tafiya ta kamfanin a lokacin aikin Hajji mai zuwa.

A nasa jawabin, mawallafin jaridar Hajj Reporters kuma kodinetan ƙungiya mai zaman kanta ta kasa kan rahotannin aikin Hajji da Ummara, Ibrahim Mohammed ya ce “mun yi sha’awar aiki da Alkauthar ne saboda ingantacciyar hidimar da kamfanin ke yi wa kwastomominsa.

Mun ga dacewar mu ba su cikakken daukar rahotanni kan ayyukan su don zama abin kwazo ba kawai a gare su ba har ma da sauran masu ba da ayyuka da hidimomi a cikin aikin Hajji”.