Za a fara yi wa maniyyatan jihar Oyo alluran rigakafi gobe

0
240

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Oyo ta bayyana cewa za ta gudanar da aikin rigakafi ga dukkan maniyyatan jihar a gobe Laraba, 17 ga Mayu, 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Sayed Malik Hamza ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, kamar yadda sanarwa daga Raji K. K, jami’in hulda da jama’a na hukumar ta bayyana.

Farfesa Malik ya yi kira ga dukkan maniyyatan da su hadu a sansanin alhazai na Olodo, Ibadan, wurin da za a gudanar da aikin rigakafin tun karfe 8 na safe.

A tuna cewa hukumar, a farkon wannan watan ta gudanar da aikin tantance lafiya da wayar da kai ga mafi yawan maniyyatan ta a fadin jihar.

Malik ya bayyana cewa aikin rigakafin zai zama wata dama ga wadanda ba su samu damar halartar aikin tantancewar ba saboda jami’an lafiya za su sake kasancewa don yi musu gwaje-gwaje.

Ya kuma bukaci wadanda ba su yi gwaje-gwajen lafiyar ba a baya da su halarci wannan atisayen, sannan kuma su lura cewa atisayen na daya daga cikin bukatu da tsare-tsare da ya wajaba kowanne maniyyaci ya cika kafin ya tashi zuwa kasa mai tsarki.

Shugaban Hukumar ya ce, “za a ba su alluran rigakafi daban-daban domin kare su daga kamuwa da cutar Polio, shawara, Sankarau da sauran cututtuka masu yaduwa daidai da bukatun kasa da kasa na tafiye-tafiye”.