Hajjin 2023: NAHCON ta sanya ranar 25 ga Mayu don fara jigilar maniyyatan Nijeriya

0
166

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta sanya ranar 25 ga watan Mayu don fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana 2023 daga Najeriya zuwa Saudiyya.

Hukumar za ta ƙaddamar da jigilar alhazan ne da alhazan jihar Nassarawa.

Shugaban hukumar ta NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da tawogar ƴan jarida ta Hajjin bana a shelkwatar ta da ke Abuja a yau Alhamis

Shugaban, wanda ya bayyana cewa tawagar ma’aikatan NAHCON za su tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar Lahadi mai zuwa domin shirya tarbar maniyyatan Najeriya, ya jaddada muhimmancin kafafen yada labarai wajen gina kasa da hadin kai.

Ya ce kafafen yada labarai na da ikon ɗaukaka, ko kuma rusa wa, ya danganta da abin da tunanin su ya ba su.

Alhaji Zikrullah ya bukaci ƴan tawogar ta ƴan jarida da su kasance masu gaskiya da adalci a cikin rahotonninsu ta hanyar yada bayanan da suka dace kafin aikin Hajji da lokacin aikin da ma bayan kammala aikin Hajji.

A nasu jawabin, kwamishinonin tsare-tsare da bincike, Shaykh Sulayman Momoh da Alhaji Nura Hassan Yakasai duk sun shawarci ƴan tawogar da su kasance jakadu na hakika na aikin jarida ta hanyar yin gaskiya da rikon amana da daidaito a cikin aikin jarida tare da bayar da rahoto na gaskiya a Najeriya da Saudiyya a duk tsawon lokacin aikin Hajji.