Babban Dara na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya jaddada kudirin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji na 2023 cikin nasara ba tare da matsala ba.
Suleiman Nuhu Kuki ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Kwanturolan hukumar shige da fice ta ƙasa, reshen jihar Katsina a dakin taro na hukumar, inji sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar, Badaru Bello Karofi ya fitar.
Babban Daraktan ya ce ya amince da gudunmawar da Hukumar Shige da Ficen ke bayar wa wajen gudanar da aikin hajji a jihar, ya kuma yi kira ga Kwanturolan da ya duba kalubalen wasu maniyyatan da ba su karbi fasfo dinsu na tafiye-tafiye ba, ta yadda hukumar za ta samu damar tsimaka musu su samu biza a kan lokaci.
Ya nuna jin dadinsa kan kokarin da kwantarolan ke yi wajen taimakawa hukumar ta samu nasarar Hajjin 2023.
Kuki ya kuma sanar da kwantarolan cewa hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina ta karbi jimillar kujerar alhazai dubu 4, 923, na aikin Hajjin 2023 daga hukumar alhazai ta kasa, NAHCON.
Tun da fari, Kwanturolan, Alhaji Muhammadu Adamu fsc ya ce makasudin ziyarar shi ne domin kara hadin gwiwar aiki da hukumar a ci gaba da kulla kyakkyawar alakar da ke tsakanin ta da hukumar shige da fice ta jihar Katsina.
Kwanturolan ya yi alkawarin duba lamarin tare da ba da tabbacin cewa rundunar ta samu isassun takardun fasfo domin maniyyatan jihar Katsina.