Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Kano na sanar da Maniyyatan Jihar cewa za’a rufe bitar alhazai ta kullum- kullum a ranar Litinin, 22ngs watan Mayu.
A wata sanarwar daga Matemakiyar Daraktan Ilmantarwa da wayar da Kai Kuma Kakakin hukumar, Hadiza Abbas Sanusi ta ce za a rufe bitar a gaba daya cibiyoyi 32 a faɗin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa bayan rufe bitar, za kuma a yi gangamin gwajin lafiya na aikin hajji a aikace a Sansanin alhazai na Jihar Kano daga ranar Laraba, 24 ga watan Mayu,2023 da misalin karfe 10 na safe.