Hajjin bana: Za a fara jigilar alhazan Kano ranar 25 ga Mayu — Danbatta

0
912

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Mohammadu Abba Danbatta ya ce za a fara jigilar maniyyatan Kano a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Da ya ke zantawa da manema labarai a yau Juma’a, Danbatta ya bayyana cewa, jirgin Max Air ne zai yi jigilar maniyyatan, inda ya ce zai fara da maniyyata 550 daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano zuwa filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah.

Danbatta ya ƙara da cewa za a kwashi maniyyatan Kano ɗin ne sa’o’i kadan bayan kaddamar da jirgin farko na jigilar Hajjin bana, wanda zai debi alhazan Jihar Nasarawa.

Dambatta ya ce rukunin na biyu da na uku za su tashi ne a ranakun 27 da 29 ga Mayu, duk a jirgin Max Air.

Ya yi kira ga maniyyatan da su kasance cikin shiri, inda ya hore su da su zama masu da’a da bin dokokin kasa yayin zaman su a ƙasa mai tsarki.