Hajjin bana: Maniyyaciya da ga Jihar Nassarawa ta rasu

0
196

Wata mata mai niyyar zuwa aikin Hajjin bana a jihar Nassarawa, Hajiya Aisha Yahya Sule ta rasu.

Wata mota ce ta kaɗe marigayiya Aisha yayin da ta ke tsallaka titi bayan kammala gwajin lafiya da allurar rigakafin tafiya zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar Alhazai ta Jihar Nassarawa, karkashin shugabancin Malam Idris Ahmad Almakura ta bayyana kaɗuwa da alhini bisa rasuwar maniyyaciyar.

Almakura ya ce rasuwar Aisha wani rashi ne mai ban tsoro da bakin ciki.

A sanarwar da ya fitar ga manema labarai a garin Lafiya, Almakura ya yi wa iyali da ƴannywan marigayiyar ta’aziyya tare da addu’ar Allah Ya yi mata rahma.

Hajj Reporters ta rawaito cewa tuni dai aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.