Gobara ta kashe alhazan Ummara 8 a wani otal a Makka

0
179

Akalla alhazan Ummara ƴan ƙasar Pakistan takwas ne su ka rasu, yayin da shida su ka sami raunuka a wata gobara da ta tashi a wani otal da ke birnin Makkah.

Da ya ke shaida wa manema labarai game da asarar rayuka a gobarar a otal din na Makkah, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce, “muna da rahoton mutuwar ‘yan Pakistan takwas, shida kuma suka jikkata. Domin bayar da agaji ga iyalan wadanda abin ya shafa, Ofishin Jakadancin mu na Jeddah ya na tuntubar hukumomin yankin.

Rahotannin farko sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a hawa na uku na otal din Ibrahim Khalil Road.

Wata majiya ta ruwaito cewa alhazan Pakistan, Bangladesh, da sauran alhazan Umrah ne ke sauka a otal din.