DA DUMI-DUMI: Motar da ke jigilar maniyyata aikin Hajji Nassarawa zuwa Abuja ta yi hatsari

0
537

Wata motar bas mai cin mutum 18 da ke jigilar maniyyata daga jihar Nasarawa zuwa Abuja domin jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a domin aikin Hajjin 2023 ta yi hatsari a yau Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne a kusa da Kara, karamar hukumar Keffi ta jihar Nassarawa.

Har yanzu na a samu cikakkun bayanai kan hadarin ba, amma an tattaro cewa wasu mutanen da ke cikin motar sun samu raunuka.

Hajj Reporters ta rawaito cewa hukumar alhazai ta kasa za ta gudanar da bikin kaddamar da tashin alhazan hajjin 2023 tare da alhazan jihar Nassarawa a gobe alhamis.

Jaridar ta kuma samu labarin cewa motocin bas din da za su dauko alhazan jihar Nassarawa zuwa Abuja tuni suka nufi babban birnin tarayya Abuja, hakan na nufin daya daga cikinsu na iya yin hatsarin.

Cikakken labari na nan tafe