Hajjin bana: Alhazan jihar Sokoto za su fara tashi ran Juma’a

0
502

Hukumar Alhazai ta Jihar Sokoto ta ce a gobe Juma’a za ta fara jigilar alhazai zuwa Saudi Arebiya domin Hajjin bana.

Sakataren Dindindin na hukumar, Shehu Muhammad Dange ne ya bayyana haka a zanta wa da manema labarai kan shirye-shirye da hukumar ke yi na Hajjin 2023.

A cewar sa, jihar na da gurbin alhazai 5, 304 a Hajjin bana.

Ya kara da cewa hukumar ta tanadi ingantattun masaukai na Alhazan a Makka da Madinah.

Ya kuma bayyana cewa yanzu haka ana ta aikin bizar alhazai da kuma guzirin su.

Ya yi bayanin cewa an rage guzirin zuwa Dalar Amurka 700 sakamakon ƙarin kuɗin jirgi da aka samu da rikicin Sudan ya haifar.