Hajjin 2023: Za a baiwa kowanne maniyyacin Katsina guzurin dala 700 – Hukumar Alhazai

0
502

Hukumar Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar da cewa kowanne maniyyacin jihar da zai je aikin Hajjin bana zai karɓi Dalar Amurka 700, maimakon dala 800 a matsayin guziri.

Babban Daraktan hukumar, Alhaji Suleiman Nuhu Kuki ya bayyana ne hakan ga maniyyatan yayin ziyarar duba shirin allurar rigakafin mahajjata a ofishin shiryya na Daura.

Kuki ya kara haske da bayanin cewa ragin ya afku ne sanadiyyar yakin da ake a kasar Sudan, wanda ya haddasa yin dogon kewaye ta kasar Misra, da ya kara tsawon tafiyar da kimanin saka da awanni biyu.

A wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na hukumar, Badaru Bello Karofi, Kuki ya kuma kara jan kunnen su da su kiyaye da dokokin kasar Saudi Arabia.

Shugaban hukumar alhazan ya kuma ƙara da cewa dalilin rikicin Sudan ne ya sanya Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta yanke shawarar rage wa dukkan Alhazan kasar nan Dala 100 domin cika karin kudin da kamfanonin jiragen sama suka ne ma.

Daga karahe Babban Daraktan, tare da daraktocinsa sun duba yadda ake yi wa maniyyatan allura tare da ba su kananan jakankuna da uniform don shirin tafiya a rukuni na farko.