Hajjin 2023: Rukunin farko na maniyyatan Kano za su tashi ranar 3 ga watan Yuni

0
642

Rukunin farko na Maniyyatan jihar Kano za su fara tashi zuwa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar, Muhammad Abba Dambatta ne ya sanar da hakan a wajen taron gwajin aikin Hajji ga maniyyatan jihar a yau Asabar a sansanin alhazai.

Bayan gwajin ne kuma Dambatta ya ƙaddamar da rabon jakukkunan hannu ga maniyyatan, inda ya ce duk wani shiri da ake buƙata, da gwaje-gwajen lafiyar maniyyata ya kammala sai jiran tashi kawai zuwa ƙasa mai tsarki.

Ya yi godiya ga Allah da kuma gwamnan Abdullahi Umar Ganduje bisa bashi dama ya shugabanci Hukumar tsawon shekaru shida.

Sannan ya yaba da yi wa ma’aikatan sa godiya bisa hadin kai da su ka bashi wajen sauke nauyin da ke kansa.

Ya kuma rufe da godewa akhazai bisa da’a da hadin kai da su ke bashi.