Hukumar Alhazai ta Jihar Ogun (OGMPWB), ta ce rukunin farko na maniyyatan 1,234 da jami’ai uku za su bar Najeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana a ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023.
Shugaban hukumar, Alhaji Salau Dauda ne ya bayyana haka yayin bitar ƙarshe da aka shirya wa maniyyatan a ranar Alhamis a hukumar da ke Oke-Ilewo, Abeokuta, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye.
Salau ya horo maniyyatan da sunayensu ya fito a cikin masu tafiyar da su zauna cikin shiri gudun kada su rasa jirgin da aka ƙayyade zai yi jigilarsu a ranar da aka tsayar, yana mai cewa hukumar ta yi tsarin da za a cimma nasara wajen jigilar maniyyatan.
A cewarsa, “Mun kintsa sarai don gudanar da ayyukan Hajji cikin nasara. Gwamnatinmu ta damu matuƙa game da walwalar maniyyatanmu, don haka muka yi kyakkyawan shiri domin tabbatar da komai ya gudana cikin nasara.”