Hajj 2023: Kusan maniyyata 900 na Plateau sun isa ƙasa mai tsarki — Shugaban Hukumar Alhazai

0
551

Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Plateau, Barista Auwal Abdullahi ya bayyana cewa an kwashi kusan akhazai 900 na jihar zuwa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Ya ce an kwashi alhazan ne a sahu biyu na jigilar aikin Hajjin bana, inda ya kara da cewa an sauke su je a filayen jirgin sama na Madina da Jeddah.

Abdullahi ya nuna kwarin gwiwa cewa za a kwashe sauran alhazan jihar a kan lokaci.

Shugaban ya kuma yaba da yadda aikin kasar alhazan ke tafiya cikin nasara, inda ya yabawa Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON kan shirye-shirye masu inganci da ta yi da ya sanya ake samun nasara a jigilar alhazai.